Gwamna Dauda Ya Bayyana Sabon Mataki Kan Batun Sulhu da ‘Yan Bindiga

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta shirya yin sulhu da ‘yan bindiga. A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, gwamnan ya tabbatar da cewa suna ladabtar da wasu jami’an tsaro da suka yi kuskure.

Dauda Lawal ya ce an samu ci gaba a fannin tsaro a jihar, duk da cewa har yanzu akwai wasu yankuna da ke buƙatar kulawa ta musamman. Ya bayyana cewa jihar ba ta amince da sulhu da masu laifi, sai dai wadanda suka miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba.

Gwamnan ya kara da cewa an bayar da motoci guda 140 ga hukumomin tsaro don inganta ayyukansu. Hakanan, ya bayyana cewa gwamnonin Arewacin Najeriya na shirin haduwa don tattauna hanyoyin magance matsalar rashin tsaro.

Gwamna Dauda ya ce, “Idan Zamfara na ɗaukar mataki amma Katsina ko Sokoto ba su yi ba, ‘yan bindiga za su koma can.” Wannan na nuni da bukatar hadin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *