Gwamna Buni Ya Kafa Sabuwar Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi a Jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bi sahun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen kafa sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobi a jihar. Wannan mataki na nufin inganta harkar kiwo a jihar, wadda ta shahara a fannin.

A cikin sanarwar da sakataren yaɗa labarai na gwamnatin jihar, Alhaji Shuaibu Abdullahi, ya fitar, gwamna Buni ya umarci sakataren gwamnatin jihar da kwamishinan noma su tsara ayyukan da sabuwar ma’aikatar za ta gudanar. Ya kuma umarci su samar da ofis da ma’aikata domin tabbatar da cewa an fara aiki cikin gaggawa.

Wannan sabuwar ma’aikatar na daga cikin sabbin ma’aikatu uku da gwamna Buni ya kafa tun lokacin da ya karbi mulki a jihar, wanda hakan ya bayyana nufin sa na inganta rayuwar al’ummar jihar ta hanyar samar da sabbin hukumomi da ma’aikatu.

A cikin shekaru shida da suka gabata, gwamna Buni ya kafa ma’aikatar jin ƙai da walwala da ma’aikatar samar da ayyukan yi, tare da samar da hukumomi 13. Wannan sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobi na kara jaddada kudirin gwamna Buni na inganta tattalin arzikin jihar Yobe.

A halin yanzu, gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyuka da zasu inganta rayuwar al’ummar jihar, tare da bayar da goyon baya ga manoma da masu kiwo.