Gwamna Bala Ya Nuna Damuwarsa Kan Wahalar Rayuwa a Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan halin ƙuncin rayuwa da al’umma ke ciki bayan sun zaɓe su ne domin kawo sauyi mai amfani. A cikin sakon da ya fitar na taya mabiya addinin Kirista murnar bikin Kirisimeti, Gwamna Bala ya ce gwamnatinsa na iya bakin ƙoƙarinta wajen magance halin tsadar rayuwar da mutane ke ciki.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar Bauchi da su ci gaba da hakuri a yayin da gwamnatinsa ke aiki tuƙuru don rage wahalhalun da suke fuskanta. Ya ce, “Ina kira gare ku duka da ku ci gaba da yin hakuri, yayin da muke kokarin kawo karshen wannan matsin tattalin arzikin da ake ciki.”

Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki don inganta rayuwar al’umma, musamman ma a fannin tattalin arziki, inda ya bayyana cewa suna fuskantar kalubale ne daga hauhawar farashi da talauci. Ya ce, “Mun damu sosai duba da mutanen da suka zaɓe mu domin mu aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwarsu.”

Gwamna Bala ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don magance wahalhalun da al’umma ke fuskanta a yanzu, tare da fatan cewa za a samu canji mai kyau a nan gaba. Wannan bayyana damuwa daga gwamnan na daga cikin kokarin sa na tabbatar da cewa al’umma suna da ingantaccen rayuwa.