
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya samu goyon baya daga wata ƙungiya ta matasan kiristoci da dattawa a jihar, wanda suka bayyana goyon bayansu ga shirin gwamnan na neman takarar shugaban kasa a 2027. Wannan bayani ya fito ne daga taron manema labarai da shugabannin kungiyar suka gudanar a Bauchi.
A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin kungiyar, Joel Joshua da Ɗanladi Audu, sun jaddada cewa suna marawa gwamnan baya a duk wani ɗan takarar da zai gaje shi a kujerar gwamna, da kuma wanda zai tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2027.
Kungiyar ta yaba wa Bala Mohammed bisa shugabancinsa na adalci da hadin kai, inda suka ce ya tabbatar da hadin kan kabilu da addinai a cikin jihar. Sun bayyana cewa, “Gwamna Bala ya kasance mai girmama dukkan addinai, kuma wannan yana daga cikin dalilan da muke goyon bayansa.”
Gwamnan ya samu yabo daga kungiyar bisa kokarinsa na inganta tsaro da samar da ingantaccen shugabanci a shekarun da ya shafe yana mulkin Bauchi. Ƙungiyar ta bukaci gwamnan da ya saurari kiraye-kirayen da ake masa daga sassa daban-daban na kasar, ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka cancanta don jagorantar Najeriya a wannan lokaci.
Kungiyar ta kuma yi alkawarin marawa gwamnan baya tare da fatan cewa zai zabi wanda ya dace don ci gaba da kyawawan ayyukan da yake yi. Wannan goyon baya na ƙungiyar kiristoci na daga cikin kokarin da ke nuna yadda gwamna Bala Mohammed ke samun goyon baya daga al’umma a jihar Bauchi.