
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana ranar Juma’a, 17 ga Janairu, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna jihar damar gudanar da zaben ciyamomi. Wannan mataki na gwamna ya biyo bayan shirin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ondo (ODIEC) na gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 18 ga watan Janairu.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ebenezer Adeniyan, ya fitar, an bayyana cewa an dauki wannan matakin don tabbatar da cewa ma’aikata da sauran al’umma sun samu damar kada kuri’unsu cikin lumana. Gwamna Aiyedatiwa ya yi kira ga dukkanin al’umma su ba da hadin kai domin ganin an gudanar da zaben cikin tsari da zaman lafiya.
Sai dai, jam’iyyar PDP ta sanar da janyewarta daga zaben kananan hukumomin saboda rashin amincewa da tsarin zaben da hukumar ODIEC ke gudanarwa. Daraktan yada labarai na PDP, Leye Igbabo, ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke shawarar janyewa bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyar.
Hukumar zabe ta jihar ta tabbatar da cewa ficewar PDP daga zaben ba zai shafi tsarin zaben da aka shirya ba, inda ta ce har yanzu akwai sauran jam’iyyun siyasa guda 10 da za su shiga zaben.
A wani bangare, rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar da hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 6 na safe zuwa 4 na yamma a ranar Asabar don dalilai na tsaro. Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Wilfred Afolabi, ya bayyana cewa wannan mataki yana da muhimmanci don tabbatar da zaman lafiya yayin zaben.
Zaben kananan hukumomi a jihar Ondo na da matukar muhimmanci, kuma jama’a na sa ran ganin yadda wannan zabe zai gudana tare da daukar matakai na tsaro da suka dace.