Gwamna Abba Ya Umarta Masarautu Su Shirya Hawan Sallah Duk da Hukuncin Kotu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin cewa masarautun jihar guda hudu su shirya gudanar da hawan Sallah karama, duk da umarnin kotu da ya dakatar da aiwatar da wasu tsare-tsare na masarautu. Wannan umarni ya fito ne a lokacin taron buda baki na Ramadan da aka gudanar tare da sarakuna a Fadar Gwamnatin Kano.

Gwamna Abba ya bayyana cewa hawan Sallah na da matukar muhimmanci wajen nishadantar da al’umma da kuma inganta al’adun gargajiya. Ya ce jama’a na sa ran ganin bikin Sallah, suna sanya sababbin kaya da zuwa tituna domin kallon sarakunan su akan doki.

Ya tabbatar da cewa dukkan hukumomin tsaro na jihar za su kasance cikin shiri don samar da tsaro ga al’umma yayin gudanar da bukukuwan. Abba ya jinjinawa sarakunan jihar bisa kyakkyawar dangantaka da suka nuna, yana mai cewa wannan yana kara girmama tsarin masarautu a jihar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da majalisar masarautar Kano a watan Afrilu, inda za a bayyana dokoki da ka’idojin da suka shafi majalisar. Wannan matakin na gwamna Abba ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, wanda ya sa mutane ke ta tattaunawa kan tasirin wannan umarni a harkokin siyasar jihar.