
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Salisu Mustapha, bisa zargin cire kudi daga albashin ma’aikata ba bisa ka’ida ba.
An bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook. Sanarwar ta nuna cewa gwamna Abba ya nada Malam Umar Muhammad Jalo a matsayin sabon mukaddashin shugaban ma’aikatan, yayin da ake gudanar da bincike kan zargin.
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, wanda aka ba shi kwanaki bakwai don gano gaskiyar lamarin. Gwamna Abba ya yi alkawari cewa, duk wanda aka samu da laifi na zabtare albashin ma’aikatan jihar zai fuskanci hukunci.
Ya ce, “Gwamnatina ba za ta yarda da wata badakala ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani.” Wannan mataki na gwamna ya zo ne a lokacin da ake ta fama da rahotannin rashin biyan albashi da kuma rage albashin wasu ma’aikata.
Malam Umar Muhammad Jalo, wanda aka nada sabon mukaddashin shugaban ma’aikatan, yana da alhakin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki har sai an kammala binciken. Gwamnan ya jaddada cewa yana da niyyar ganin an yi wa ma’aikatan jihar adalci da tabbatar da cewa an biya su haƙƙoƙinsu.
Wannan mataki ya samu goyon bayan jama’a, inda wani matashi a Kano, Bashir Abdullahi El-Bash, ya bayyana cewa akwai bukatar gudanar da bincike cikin gaskiya don ganin an hukunta masu laifi. Ya kuma yi kira ga gwamnatin cewa a dawo da kudaden da aka cire daga albashin ma’aikatan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar da gaskiya da adalci a cikin harkokin ma’aikatan jihar.