
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana damuwarsa game da rahotannin da ke nuna cewa wasu ma’aikatan gwamnati na fuskantar yankewar albashin su. A cikin wata sanarwa mai karfi da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana wannan hali a matsayin cin zarafi da take hakkin ma’aikatan da suke fafutuka domin samun na kansu.
Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike da nufin gano masu hannu a cikin wannan aikin zalunci. Ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta amince da kowanne irin zalunci ga ma’aikatan gwamnati ba, kuma duk wanda aka kama da hannu a wannan aika-aika zai fuskanci hukunci mai tsanani.
A ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen wannan matsala, gwamnan ya umarci kwamitin da ya gudanar da bincike kan asalin matsalar, wanda ya shafi tsarin biyan albashi na jihar daga watan Oktoba 2024 zuwa Fabrairun 2025. Kwamitin zai tantance ma’aikatan da abin ya shafa tare da bayar da shawarwari kan matakan da za a ɗauka don gyarawa.
Kwamitin binciken yana da mambobi bakwai, wanda Hon. Abdulkadir Abdussalam ya jagoranta, tare da haɗin gwiwar ƙwararru a harkar kudi da tsarin biyan albashi. An ba su wa’adi na kwanaki bakwai domin kammala bincike da gabatar da rahoto kan wadanda ke da alhakin aikata laifin.
Gwamna Abba ya tabbatar wa ma’aikatan cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare hakkinsu da tabbatar da cewa ana biyan albashi akan kari. Wannan mataki na gwamnan na nufin dawo da adalci da inganta tsarin biyan albashi a jihar Kano.