
Dan wasan Super Eagles na Najeriya, Ademola Lookman, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika na shekarar 2024 a taron da aka gudanar a Marrakech, Morocco. Wannan nasara ta bashi damar ficewa a matsayin zakaran Afrika bayan ya kayar da wasu fitattun ‘yan wasa kamar Achraf Hakimi da Simon Adingra.
Lookman ya bayyana yadda ya yi fama da kalubale da dama kafin samun wannan gagarumar nasara a rayuwarsa. Ya tuna da wani babban kuskure da ya yi a shekarar 2020 lokacin da yake buga wa Fulham wasa a gasar Premier League. A lokacin, ya yi yunkurin jefa bugun fanareti na salon Panenka, wanda ya gaza sakawa a raga, lamarin da ya jawo suka daga bakin kocinsa, Scott Parker, da sauran jama’a.
Scott Parker ya ja kunnen Lookman, yana mai cewa, “Ba za ka iya samun nasara a bugun fanareti da irin haka ba. Duk da cewa matashi ne mai koyo, ya kamata ya dauki darasi daga wannan kuskure.”
Duk da wannan kuskure, Lookman ya ci gaba da dagewa har ya kai matsayin zakaran dan kwallon Afrika. Ya bayyana cewa, “Shekaru hudu da suka gabata, na gaza a idon duniya. Amma yanzu, bayan shekaru hudu, na zama gwarzon dan kwallon Afrika.” Wannan kalaman na nuni da yadda ya tsallake kalubalen da suka fuskanta a baya.
Lookman ya yi godiya ga Allah, shugabanni, abokan wasansa, da duk wadanda suka ba shi goyon baya a wannan tafiya. Ya ce lashe kyautar abin alfahari ne ga kansa, iyalansa, da kasarsa Najeriya, kuma wannan zai karfafa guiwar matasan Afrika masu burin samun nasara a rayuwa.
A cikin jawabin sa, Lookman ya shawarci matasa da kada su bari kurakuransu su hana su cimma burinsu. Ya nuna cewa wahalar da ya sha tana da matukar amfani, kuma yana da mahimmanci su ci gaba da fafutuka don samun nasara a rayuwa.
Wannan nasara ta Lookman tana nuni da irin bajintar da ‘yan Najeriya ke yi a fagen wasanni, tare da fatan ganin karin nasarorin a nan gaba.