
Wata mummunar gobara ta tashi a asibitin koyarwa na jami’ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso a jihar Oyo, yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Gobarar, wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, 2024, ta yi sanadiyyar lalata dukiya mai tarin yawa ta miliyoyin Naira.
Gobarar ta shafi sashin kula da ba da agajin gaggawa da hadurra na asibitin, inda ta lalata kayan ofis, littattafai, na’urorin lantarki, rufi da silin. Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe, sakamakon tsartsarin wutar lantarki daga wani ofishi.
Hukumomin asibitin sun yi gaggawar fitar da majinyata 16 daga sashin a lokacin da gobarar ta tashi, domin kaucewa asarar rayuka. Jami’in hulɗa da jama’a na asibitin, Omotayo Ogunleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce komai ya dawo daidai kuma an ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum a asibitin.
Wannan lamari ya jefa al’ummar jihar Oyo cikin tashin hankali, inda mutane da dama ke nuna damuwa game da irin wannan gobara a asibitin. Wasu sun yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki domin inganta tsaron asibitocin a fadin kasar nan.