
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su sami saukin rayuwa da jin daɗi a sabuwar shekarar 2025. A cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, Ganduje ya bayyana cewa alamu sun nuna cewa tsare-tsaren tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya kirkiro za su haifar da sakamako mai kyau.
Ganduje ya yi nuni da cewa, “Daga yanzu zuwa bikin Kirismeti, tattalin arzikin kasar zai daidaita kuma ya inganta.” Ya bayyana cewa, irin kyawawan halaye da fata na ci gaba da Tinubu suna zama kamar na manyan shugabannin Najeriya a baya, kamar Sardauna da Tafawa Balewa.
Shugaban APC ya bayyana cewa, duk da kalubalen da Najeriya ke fuskanta, akwai tabbacin cewa za a samu ci gaba mai ma’ana a fannin tattalin arziki a cikin shekaru masu zuwa. Ya kuma jaddada cewa, gwamnatin Tinubu ba ta da niyyar hargitsa al’umma, sai dai kawo ingantaccen sauƙi da walwala a cikin al’umma.
Ganduje ya kwantar da hankalin ‘yan Najeriya, yana mai cewa lokaci ne na shirin kyautata rayuwa a ƙasar, kuma yana da mahimmanci a shiga 2025 da kyakkyawan fata.