
A cikin wata jawabi da ya yi a ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2024, shugaban jam’iyyar APC a Najeriya, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin kwace iko a jihar Rivers a zaben gwamna na 2027. Ganduje, wanda tsohon gwamnan Kano ne, ya ce yankin Kudu maso Kudu yana da matukar muhimmanci ga APC, yana mai cewa suna bukatar goyon bayan al’umma domin cimma wannan burin.
A yayin rantsar da Cif Tony Okocha da wasu mutum 22 a matsayin shugabannin APC a jihar, Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu nasara a jihohin Cross River da Edo, kuma yanzu lokaci ya yi da za a mai da hankali kan jihar Rivers. Ya yi kira ga ‘yan APC da masu ruwa da tsaki a jihar su kara himma domin ganin jam’iyyar ta lashe zaben.
Ganduje ya ce, “Rivers ce muka sanya a gaba. Mun yi nasara a sauran jihohi, kuma yanzu lokaci ya yi da za mu karbe jihar Rivers daga hannun PDP.” Ya kara da cewa, duk da cewa PDP ta dade tana rike da jihar, akwai fata na samun nasara a wannan zabe mai zuwa.
Jawabin Ganduje ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a siyasar jihar, inda ya jaddada bukatar hadin kai da aiki tare domin ganin nasarar APC a zaben 2027.