
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya al’ummar Musulmai murnar shigowar watan azumin Ramadan tare da ba da wasu muhimman shawarwari.
A cikin saƙon da ya fitar a ranar Lahadi, Ganduje ya yi kira ga Musulmai da su mai da hankali kan taimakon talakawa da mabuƙata yayin wannan wata mai alfarma. Ya bayyana cewa Ramadan lokaci ne na jinƙai, kyauta, da ƙarfafa imani.
Ganduje ya ce, “Wannan wata yana ba mu damar komawa ga Allah, mu yi ibada da jajircewa, sannan mu taimaki waɗanda ke cikin buƙata.” Ya kuma roƙi al’ummar Musulmai da su ci gaba da yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’a, don Allah Ya ba shi hikima da ƙarfi wajen gudanar da al’amuran ƙasa.
Ya jaddada cewa, “Mu tuna da waɗanda suka fi rauni a cikin al’umma, kuma mu ƙara himma wajen gina al’umma mai haɗin kai da adalci.” Ganduje ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da aiki tukuru domin inganta walwala da jin daɗin kowa da kowa, ba tare da la’akari da addini ko asalin mutum ba.
A ƙarshe, Ganduje ya yi fatan cewa wannan Ramadan zai kasance mai alfarma ga dukkan Musulmi a Najeriya, yana mai yi musu addu’a da Allah Ya karɓi ibadunsu.