Ganduje Ya Bayyana Shirin Tattalin Arziki a Najeriya kafin 2025

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ƙara hakuri tare da yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu uziri. Ganduje ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murnar bikin Kirisimeti.

A cikin jawabin sa, Ganduje ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa za su fara ganin canje-canjen da suka kamata a fannin tattalin arziki nan da shekarar 2025. Ya ce, duk da wahalhalun da al’umma ke fuskanta, musamman na hauhawar farashin kayayyaki, akwai tabbacin cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa.

Ganduje ya jaddada cewa akwai matsaloli da dama da ‘yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da rashin tsaro, talauci, da yunwa. Ya danganta haka da cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi, wanda ya haifar da ƙarin matsaloli ga al’umma.

Ganduje ya yaba da kokarin Tinubu na inganta dimokiradiyya a Najeriya, yana mai cewa gyare-gyaren da shugaban kasar ya fara suna kawo sakamako mai kyau. Ya roki ‘yan Najeriya da su kasance masu juriya da hakuri yayin da gwamnati ke fuskantar kalubalen da ke gaban ta.

Ganduje ya yi imanin cewa tare da haɗin kai da goyon bayan al’umma, gwamnati za ta iya cimma manufofinta na inganta tattalin arziki da kawo ci gaba mai ɗorewa a Najeriya kafin shekarar 2025.