
A wani lamari mai tayar da hankali, wasu fusatattun mutane sun dauki doka a hannunsu a jihar Anambra, inda suka bankawa wasu masu karbar kudin haraji wuta. Wannan lamari ya auku ne bayan masu karbar harajin sun jawo wani mutum ya rasa ransa a kokarin karbar kudi wajen wani direba.
An ruwaito cewa lamarin ya auku ne a karshen mako a hanyar tsohuwar kasuwa, kusa da titin Venn a Egerton. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an harajin sun yi kokawa da wani direban babbar mota wajen karbar sitiyarinsa. Direban ya rasa yadda zai yi, lamarin da ya sa motar ta kwace sannan ta bugi wani mutum da ke bakin titi.
Fusatattun mutane, wadanda suka hada da masu tuka keke Napep, sun hana jami’an harajin tserewa daga wurin da lamarin ya faru. Sun lakada musu duka da abubuwa daban-daban kafin su banka musu wuta.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce mutum biyu ne suka mutu sakamakon lamarin, yayin da wasu guda hudu suka samu suka tsere. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Tochukwu Ikenga, ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Wannan lamari ya jefa al’ummar jihar Anambra cikin tashin hankali, inda mutane da dama ke sukar yadda masu karbar harajin ke aikinsu. Wasu sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki mataki kan lamarin, domin hana irin wannan abu daga sake faruwa.