
Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu kyautar motar alfarma ta N210m a ranar haihuwarsa ta 32. Wani kamfanin sayar da ababen hawa da ke da hedikwata a Dallas, Texas ne ya ba mawakin kyautar motar kirar Cadillac Escalade 600.
Gabanin samun kyautar motar, mawaki Davido ya sanar da cewa zai rabawa marayu tallafin Naira miliyan 300m a shekarar nan. Wannan sanarwa ta janyo hankalin jama’a da yawa, musamman masu tausayin marayu.
Kamfanin sayar da motocin mai suna Mr. Jay Autos LLC ya sanar da ba mawakin kyautar motar alfarmar ne a ranar Alhamis, a shafinsa na Instagram. Kamfanin ya godewa mawakin kan ci gaba da kasancewa abokin huldarsu da kuma irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.
Yana Mai cewa “A zagayowar ranar haihuwarka, kamfaninmu, MR JAY AUTOS LLC ya yanke shawarar ba ka kyautar sabuwar mota kirar Escalade 600. Muna godiya da goyon bayanka da kuma ƙaunar ka ga kamfaninmu. Muna taya ka murnar zagayowar ranar haihuwarka Oriande @davido.”
Davido Zai Ba Marayu Tallafin N300m
Jim kadan bayan sanarwar kamfanin, mawakin ya ba su amsa da cewa: “Kai! Ina kaunarku. Na gode kwarai, J!”
Kafin wannan kyautar, a kwanakin da suka gabata ne fitaccen mawakin ya sake daukar hankalin jama’a bayan sanar da shirin ba da tallafi a wannan shekarar. Ya bayyana shirin bayar da tallafin miliyoyi ga gidajen marayu a fadin Najeriya ta hannun gidaunisa ta Davido Adeleke (DAF).
“A zagayowar ranar haihuwata na bana, zan rabawa marayu tallafi, zan kuma tallafawa matasa domin karesu daga shan miyagun kwayoyi. Wannan shekarar, zan raba tallafin Naira miliyan 300. Nan gaba kadan zan sanar da cikakken bayani game da tallafin.” – Davido ya wallafa a shafinsa na X.
Martanin Jama’a
Sanarwar da Davido ya yi game da tallafin da zai bayar ga marayu ta janyo martani iri-iri daga jama’a. Wasu sun yaba masa da wannan mataki, yayin da wasu suka yi masa addu’a Allah ya saka masa da alheri.
“Allah ya saka maka da alheri, Davido. Wannan tallafin da za ka bayar zai taimaka wa marayu da yawa.” – In ji wani mai amfani da shafin X.
“Wannan shi ne abin da ake kira da ainihin taimakon al’umma. Davido, ka yi abin da ya dace.” – In ji wani mai amfani da shafin Facebook.