Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Fargaba a Zamfara: Kauyuka 50 Sun Watse Saboda Barazanar Bello Turji

Fargaba ta mamaye jihar Zamfara, inda fiye da kauyuka 50 a karamar hukumar Shinkafi suka zama kufai sakamakon barazanar da dan bindiga, Bello Turji, ya yi. Turji ya yi gargadi kan kai hare-hare a kananan hukumomi uku idan ba a saki yan uwansa da sojoji suka kama ba.

Rahotanni sun nuna cewa sama da kashi 80% na mazauna Shinkafi sun tsere zuwa garin Kaura-Namoda don samun tsaro daga hare-haren da ake zargin Turji zai kai. Wannan hijira ta faru ne bayan bidiyon da Turji ya fitar, inda ya bayyana cewa zai kai hari a Shinkafi, Zurmi, da Isah idan ba a saki Bala Wurgi, wanda aka kama ba.

Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, wani jigon APC, ya tabbatar da wannan lamari ga manema labarai a Gusau, ya kuma kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa don kare rayukan al’umma daga wannan barazana.

Wannan yanayi na rashin tsaro ya jawo damuwa a tsakanin al’umma, yayin da ake kira ga gwamnati ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.