
Hajiya Naja’atu Muhammad, fitacciyar ‘yar gwagwarmaya a siyasance a Arewacin Najeriya, ta bayyana damuwarta game da yiwuwar gwamnatin Bola Tinubu ta watsa dokar ta baci a wasu jihohi, musamman ma jihar Kano. Ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin mamaye wasu jihohi don baiwa Tinubu damar ci gaba da mulki bayan wa’adin farko.
Naja’atu ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da ta yi da tashar Premier Radio, inda ta bayyana cewa bayan samun nasara a jihar Rivers, gwamnatin Tinubu na fuskantar barazana ga zababbun shugabannin jihohi. Ta yi zargin cewa akwai wasu jihohi da gwamnatin tarayya ke son mallaka domin cimma burinta na siyasa.
Ta ce: “Kano ma abin da suka so su yi ke nan. Idan ka na jin labarin yadda ake zuzuta rigima a kan sarakuna, waye ke tayar da rigima? Waye ya damu, alhalin mutanen Kano suna harkar cinikayyar su, suna neman kudinsu?”
Hajiya Naja’atu ta yi gargadi ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen hana yunkurin amfani da dokar ta baci, wanda a cewarta, zai ci gaba da cire gwamnoni da sanatoci da ba a so. Ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani shiri da zai iya kawo cikas ga dimokuradiyya a kasar.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Kano ta fara gudanar da naɗe-naɗe a cikin gwamnatin ta, inda aka zabi matasa da dama don cike mukamai daban-daban, yayin da ake ci gaba da fargaba game da tasirin dokar ta baci a kan harkokin siyasa da zaman lafiya a jihar.