Farfesoshin Jami’ar ABU Zaria Sunyi nazari Kan  Illolin da ke cikin Kudirin Gyaran Haraji

Farfesoshin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zaria) daga Cibiyar CEDERT sun gudanar da bincike kan illolin da kudirin gyaran haraji na gwamnatin Najeriya zai iya haifarwa. Farfesa Abubakar Siddique Muhammad da Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi sun yi nazari a kan kudirorin, inda suka bayyana shawarwari da tsokaci kan tasirinsu ga tattalin arziki da zamantakewa.

Masana sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke gaggawa wajen amincewa da kudirin ba tare da tattaunawa da al’umma ba, wanda hakan zai iya haifar da matsaloli. Sun jaddada cewa karin harajin VAT daga 7.5% zuwa 15% zai jawo tashin farashin kayayyaki, wanda zai shafi talakawa a Najeriya.

Bugu da ƙari, sun yi gargadi game da yiwuwar rage karfin hukumar TETFund, wanda zai shafi tallafin ilimi, da kuma yiwuwar jawo karancin kudade ga hukumomin da ke gudanar da harkokin ilimi da fasaha a ƙasar. Farfesoshin sun ba da shawarar cewa a gudanar da tattaunawa mai kyau tare da al’umma kafin a yanke hukunci kan kudirin.

A karshe, sun kira ga majalisar tarayya da ta duba kudirin da kyau, ba tare da gaggawa ba, domin gujewa matsaloli da za su iya tasowa daga aiwatar da sabuwar doka.