Farashin Man Fetur Ya Tashi a Najeriya Bayan Sabon Karin Ɗangote

Farashin litar man fetur a Najeriya ya tashi zuwa tsakanin N1,050 da N1,150, bayan sanarwar karin farashi daga matatar Ɗangote. Wannan hauhawar farashin ya kasance sakamakon karuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Kungiyar ƴan kasuwa ta IPMAN ta bayyana cewa a yanzu haka, farashin litar man fetur ya haura N1,000 a faɗin jihohin ƙasar, sabanin yadda aka saba. Wannan ƙarin farashin ya biyo bayan matatar Ɗangote ta sanar da sabon farashi na N955 da N950 a wuraren lodin ƴan kasuwa.

A cewar rahoto daga jaridar Punch, dillalan mai sun yi hasashen cewa za a ci gaba da samun ƙari a farashin fetur a nan gaba, musamman bayan samun karin farashin ɗanyen mai wanda ya tashi zuwa dala 80 a kowace ganga. Sakataren yada labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce farashin na iya kaiwa N1,100 a Legas da N1,150 a babban birnin tarayya, Abuja.

Hakan ya jaddada cewa gwamnati ba ta da hannu a cikin wannan hauhawar farashin, inda ministan albarkatun man fetur na Najeriya ya ce yanayin kasuwa ne ke yanke farashi a yanzu. Wannan sabuwar hauhawar farashin man fetur na ƙara jaddada wahalar da al’umma ke fuskanta a Najeriya, inda aka riga an yi fama da matsalolin tattalin arziki.

Duk da haka, jami’an gwamnati sun nuna damuwa game da tasirin wannan hauhawar farashin kan al’umma, suna mai fatan samun hanyoyin magance wannan batu a nan gaba.