
Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis, ya bayyana yadda ya tsira daga harin kunar bakin wake sau biyu yayin ziyarar sa a kasar Iraqi a watan Maris na 2021. A cikin wani littafi da zai fito nan gaba, Fafaroma ya bayyana cewa an sha gargadi a kan yiwuwar kai masa hari, wanda ya sa ya yi tunanin dakatar da ziyarar.
Fafaroma ya bayyana cewa, ko da yake an yi masa gargadi, ya ga dacewar ya ci gaba da tafiya saboda muhimmancin ziyara ga al’ummar Iraq. Harin ya faru ne lokacin da wata mata dauke da bama-bamai ta nufi Mosul da nufin kai hari a lokacin ziyarar sa.
Jami’an tsaron Iraqi sun yi nasarar dakile yunkurin ta, inda suka kashe maharan kafin su kai ga kaddamar da harin. Fafaroma ya shaidawa duniya cewa, duk da fargabar da wasu suka nuna masa, ya yi imani cewa ziyarar ta kasance mai matukar muhimmanci ga zaman lafiya da hadin kai a yankin.
Ziyarar ta Fafaroma a Iraqi ta kasance mai tarihi, inda aka gudanar da ita cikin tsaro sosai, kuma ta kasance tafiyar farko da ya yi cikin watanni 15. Wannan lamari ya jawo hankalin duniya game da kalubalen tsaro da ke fuskantar kasashen da ke fama da rikicin addini da na siyasa.