Fadar Shugaban Kasa Ta Dauki Zafi kan Zazzafar Adawa da Kudirin Haraji daga Arewa

Fadar shugaban kasa ta bayyana rashin jin dadin ta game da yadda wasu ke sukar kudirin haraji da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar. Hadimin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana cewa kudirin yana da muhimmanci ga ci gaban ƙasar.

Dare ya shawarci masu adawa da kudirin da su zauna su tattauna, maimakon suyi sukar sa. Ya bayyana cewa:

“Matukar majalisa ta amince da kudurin, zai zama guda daga cikin manyan dokokin da ƙasa a wannan lokaci.”

Fadar shugaban kasa ta karyata zargin cewa kudirin zai cutar da Arewa, tana mai cewa kudirin zai amfanar da dukkanin mazauna Najeriya. Sun bayyana cewa:

“Kamata ya yi mu yi aiki tare wajen inganta wannan doka, domin jama’a su ci moriyarta.”

A wani labarin, wasu daga cikin ‘yan majalisar da ke Kano sun bayyana cewa ba za su amince da kudirin da zai cutar da al’umma ba. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wannan adawa.

Fadar shugaban kasa ta yi kira ga tattaunawa da muhawara a maimakon adawa, tana mai cewa wannan zai kai ga mafita da za su amfanar da kowa.