
A ranar 29 ga Maris, 2025, Fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, ta fitar da sanarwa ga al’ummar Musulmi, tana tunatar da su game da fara duban jinjirin watan Shawwal. Kwamitin ganin wata ya bukaci duk wanda Allah ya sa ya ga watan ya tura rahoton sunansa, wurin da ya ga watan, ga lambobin da aka bayar: 08020878075 da 09096369117.
Masana ilimin taurari sun bayyana cewa yana da wahala a ga jinjirin watan Shawwal a yau, amma sun yi wa al’umma gargaɗi su kasance cikin shiri. A cikin sanarwar, an shawarci mutane su fita cikin rukuni don tabbatar da sahihancin ganin watan.
Sarkin Musulmi ya umarci jama’a su fara duban watan Sallah bayan faɗuwar ranar yau, wanda hakan na nuna cewa ana sa ran za a yi idin ƙaramar sallah ne a ranar Lahadi, 30 ga Maris ko kuma ranar Litinin, 31 ga Maris, 2025. Kwamitin ya yi addu’a da fatan Allah Ya amshi ibadun da aka yi a cikin watan Ramadan.