Fabian Ozoigbo Ya Sauya Sheka Daga LP Zuwa APC, Yana Yabawa Tinubu

Tsohon jigo a jam’iyyar Labour Party (LP) kuma na hannun daman Peter Obi a zaben 2023, Fabian Ozoigbo, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ozoigbo, wanda ya jagoranci bangaren dabarun sufuri na LP a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda irin kokarin da Shugaba Bola Tinubu ke yi na gyara tattalin arzikin kasa.

Da yake zantawa da manema labarai a Awka ranar Laraba, Ozoigbo ya ce a matsayinsa na tsohon dan adawa, ya yi tsammanin rushewar tattalin arziki bayan cire tallafin man fetur. Sai dai, ya ce ya yi mamakin yadda Shugaba Tinubu ya samu nasarar daidaita tattalin arzikin duk da kalubalen da ake fuskanta.

“A matsayina na dan adawa, na zaci tattalin arzikin zai rushe bayan cire tallafin mai, amma abin mamaki, tattalin arzikin yana kan mizani mai kyau,” in ji Ozoigbo. Ya kara da cewa, “Na yanke shawarar komawa cikin gwamnatin da ke kokarin daidaita tattalin arziki domin bayar da tawa gudunmawar.”

Ozoigbo ya kuma zargi LP da rashin gaskiya, yana mai cewa jam’iyyar ta nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana.

Ya bayyana cewa ya gamsu da dan takarar gwamna na APC a Anambra, Prince Nicholas Ukachukwu, tare da bayyana cewa shigowar Sanata Uche Ekwunife cikin jam’iyyar zai kara karfafa APC a zaben gwamna mai zuwa.  “Fitowarsa (Ukachukwu), tare da ayyukan jin kai da ya dade yana yi, sun fara jawo hankalin mutane, musamman ‘yan kasa masu matsakaicin hali. Ni da mutanena muna son mu kasance cikin wannan tafiya,” in ji Ozoigbo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *