
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya bayyana damuwarsa game da wasu manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa suna da yiwuwar jefa manoma cikin talauci. El-Rufai ya yi wannan bayani ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise TV.
A cewarsa, shirin shigo da abinci daga ƙasashen waje na iya haifar da matsaloli ga harkokin noma a Najeriya, yana mai cewa wannan tsarin na shigo da abinci zai lalata harkar noma ta cikin gida. “Ba za ka iya magance matsalar tashin farashin kayan abinci ta hanyar lalata harkar noma a cikin gida ba,” in ji El-Rufai.
El-Rufai ya yi nuni da cewa duk da yana goyon bayan wasu manufofin gwamnatin, tsarin aiwatar da su ba daidai ba ne. Ya ce, “Matsalolin da aka gaji daga gwamnatin baya sun shafi harkokin tattalin arziki, amma yanzu muna da damammaki don inganta su.”
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa shigo da abinci daga ƙasashen waje ba zai magance hauhawar farashin kaya ba, sai dai yana jefa manoma cikin fatara. “Kodayake wannan yana iya rage farashin abinci, amma manoma za su shiga cikin talauci saboda ana tilasta musu yin gogayya da kayayyakin noma daga ƙasashen waje,” ya kara da cewa.
El-Rufai ya ce yana tattaunawa da wasu manyan jami’an gwamnati kan wannan batu, inda yake ba su shawarwari a sirrance. Ya yi kira ga gwamnati da ta duba ingancin mutanen da aka ba su ragamar aiwatar da waɗannan sauye-sauyen.
Wannan furuci na El-Rufai ya jawo martani daga jam’iyyar APC, inda wasu shugabanni suka bayyana cewa tsohon gwamnan yana jin haushi ne saboda rashin samun buƙatunsa a cikin gwamnatin Tinubu.