Dr. Usman Bugaje Ya Soki Gwamnatin APC Kan Rashin Inganci

A cikin wata tattaunawa da aka yi a gidan talabijin na Arise, tsohon jigo a kungiyar dattawan Arewa, Dr. Usman Bugaje, ya yi wankin gaban gwamnatin APC, yana mai zargin cewa tsarin shugabancin karba-karba a Najeriya ba ya haifar da ingantaccen ci gaba.

Bugaje ya bayyana cewa gwamnatin APC, tun daga mulkin Muhammadu Buhari har zuwa na Bola Ahmed Tinubu, ta jefa Najeriya cikin mawuyacin hali, inda ya ce sun kasa magance matsalolin da suka addabi kasar. Ya jaddada cewa tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu ba ya kawo wani ci gaba, yana mai cewa lokaci ya yi da za a daina wannan tsarin.

A cewarsa, “Mun gwada wannan tsarin na karba-karba, amma Najeriya na kara tabarbarewa.” Ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su mayar da hankali kan cancantar shugabanni maimakon yanki ko kabila, domin kawo ci gaba mai inganci.

Bugaje ya bayyana cewa manyan alamomin ci gaban kasa kamar ilimi da kiwon lafiya sun tabarbare, yana mai bayyana cewa dimokuradiyyar da ake yi a yanzu ta sabawa ainihin manufarta. A cewarsa, idan har ana son ci gaban kasa, to ya zama dole a daina fifita yankin ko addini wajen zaben shugabanni.

Hakanan, ya soki dukkan jam’iyyun siyasa a Najeriya, yana mai cewa ba kawai APC ce ta gaza ba, har da PDP, inda ya ce babu wani canji da aka samu tun daga lokacin da APC ta karbi mulki. Bugaje ya ƙara da cewa Najeriya tana buƙatar sabon tsarin mulki wanda zai kawo shugabanni nagari.