Donald Trump Ya Tono Badakalar COVID-19, Ya Yi Barazanar Ficewa daga WHO

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da shirin ficewar Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), yana zargin hukumar da gazawa wajen magance cutar COVID-19. Wannan mataki na Trump ya zo ne bayan ya bayyana damuwarsa game da tasirin siyasa da WHO ke yi da kuma yadda hukumar ke neman kuɗaɗe daga Amurka fiye da sauran ƙasashe.

Trump ya yi wannan sanarwa ne a lokacin da ya rattaba hannu kan dokar ficewa daga WHO, jim kadan bayan rantsar da shi a wa’adi na biyu. Ya zargi hukumar da rashin gamsasshen aiki a wajen yaki da COVID-19 da sauran matsalolin lafiya a duniya.

Hukumar WHO ta bayyana damuwarta game da ficewar Amurka, wacce ita ce babbar mai bayar da gudummawa ga hukumar, tana mai fatan samun tattaunawa domin gyara lamarin. Masana sun bayyana cewa ficewar Amurka na iya barazana ga shirye-shiryen WHO na yaki da cututtuka kamar tarin fuka da HIV/AIDS.

Ficewar Amurka, wadda za ta fara aiki bayan watanni 12, na nufin dakatar da dukkan gudummawar kudi da dangantakar aiki da hukumar. Wannan lamari na iya kawo cikas ga aikace-aikacen kiwon lafiya na WHO a sassa daban-daban na duniya.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafawa WHO wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya maimakon raunana su. Wannan al’amari yana jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin kasashen duniya da masana kiwon lafiya, wanda ke nuna tasirin ficewar Amurka ga lafiyar al’ummomi a duniya.