
Dattawan jihar Rivers sun yi kira ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya nemi gafarar kalaman da ya yi wa tsohon gwamna, Dr. Peter Odili. Sun bayyana cewa kalaman Wike sun sabawa dabi’un girmama dattawa da mutunta su, wanda jihar Rivers ta yi kaurin suna da shi.
Dattawan, ciki har da tsohon gwamna Celestine Omehia da Uche Secondus, sun fitar da takarda inda suka bayyana rashin jin dadinsu kan kalaman Wike. Sun ce kalaman sun zargi Dr. Odili da rashin tsayawa takarar shugaban kasa, wanda suka ce ba gaskiya ba ne.
A cewarsu, Dr. Odili ya yi biyayya ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wanda ya bukaci ya janye takara domin daidaito tsakanin Arewa da Kudu. Dattawan sun ja kunnen Wike, suna mai cewa kalamansa ba su dace da mutuncin tsohon gwamna ba.
A karshe, dattawan sun bukaci Wike da ya bada hakuri ga Dr. Odili kan kalamansa, suna mai cewa wannan matakin zai dawo da martabar Wike da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar Rivers.