
Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bayyana damuwarta kan gyaran haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta gabatar, inda ta bukaci shugaban ya janye kudurorin da aka gabatarwa majalisa. Dattawan sun zargi gwamnatin da yin kama-karya wajen tsara dokokin haraji, tare da hana al’umma furta ra’ayoyinsu.
Jagoran kungiyar, Al-Amin Daggash, ya bayyana cewa karin harajin VAT da aka shawarci gwamnati gudanar da shi zai yi illa ga yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya. Ya jaddada cewa tattaunawar kan gyaran haraji bai kamata ya zama tsakanin Arewa da Kudu kawai ba, amma ya kamata a gudanar da ita tsakanin dukkan ‘yan Najeriya.
Kungiyar NEF ta soki gwamnatin Tinubu kan rashin tuntubar kwararru da al’umma kafin tsara kudirorin gyaran haraji. Daggash ya bayyana cewa suna goyon bayan gyare-gyare masu amfani, amma suna bukatar su kasance tare da gaskiya da adalci.
Haka zalika, dattawan Arewa sun yi kiran ga gwamnati da ta dakatar da karin haraji har sai an tabbatar da farfadowar tattalin arziki, inda suka bukaci a sake duba dokar tare da tattaunawa domin warware matsalolin da aka gano.
Wannan mataki na dattawan ya jaddada cewa gwamnatin na bukatar ta bai wa duk ‘yan Najeriya damar fadin ra’ayoyinsu ba tare da tsangwama ba, domin inganta tsarin mulki da zamantakewar al’umma.