
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya yi zargin cewa wasu ‘yan ba-ni-na-iya sun karɓe ragamar mulki bayan nasarar da Muhammadu Buhari ya samu a zaben 2015. A wata hira da ya yi, Dalung ya bayyana cewa waɗanda suka yi yaƙin neman zaɓen Buhari sun rasa damar yin tasiri a mulkinsa.
Dalung ya bayyana cewa, bayan Buhari ya lashe zaɓe, wasu mutane da ba a san da su ba suka fara ware waɗanda suka yi yaƙin neman zaɓensa gefe. Ya ce, lokacin da aka bayyana Buhari a matsayin wanda ya yi nasara, ya kasance tare da shi a ofishinsa, amma an hana shi shigowa cikin gidan.
A cewarsa, ya kira wasu mutane kafin a ba shi damar shiga, daga wannan lokacin ne ‘yan ba-ni-na-iya suka karɓe iko da mulkin Buhari. Dalung ya ce wannan ya sa mulkin ya kasance bisa son zuciya na wasu, wanda hakan ya jawo matsaloli a cikin gwamnatin.
Ya ci gaba da cewa, tun daga lokacin da ‘yan ba-ni-na-iya suka karɓe mulki, ba su ba da damammaki ga waɗanda suka yi aiki tukuru domin ganin Buhari ya ci zabe ba. Wannan ya haifar da rudani a cikin jam’iyyar APC, wanda a yanzu haka ta shiga cikin rikici.
Dalung ya koka kan yadda APC ta canza daga yadda aka kafa ta, inda ya ce a yanzu al’amura sun rikice. Wannan furuci na Dalung na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan halin da jam’iyyar APC ke ciki da kuma matsalolin da suka shafi gwamnatin Buhari.