
Kamfanin matatar Aliko Dangote ya sanar da dakatar da sayar da man fetur da naira na ɗan lokaci. Wannan matakin ya biyo bayan wasu matsaloli da suka shafi musayar kuɗi a kasuwar Najeriya.
Dangote ya bayyana cewa, har yanzu ba su samu isasshen danyen mai da aka kayyade da naira daga NNPC ba. Wannan ya sa kamfanin ya yanke shawarar dakatar da sayar da mai har sai an samu daidaito tsakanin kudaden da ake samu da kuma farashin danyen mai a kasuwa.
A cikin wasiƙar da kamfanin ya aike wa ‘yan kasuwa, an bayyana cewa, “Mun yanke shawarar dakatar da sayar da man fetur da Naira na ɗan lokaci, wannan mataki ne da ya zama dole don guje wa rashin daidaito tsakanin kuɗin shiga da kuɗin sayan danyen mai, wanda yanzu haka ana biya da dalar Amurka.”
Kamfanin ya musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa dakatarwar ta faru ne saboda zamba a tikitin lodin kaya. Dangote ya tabbatar wa al’umma cewa suna da niyyar ci gaba da bauta wa kasuwar Najeriya yadda ya kamata da kuma nagarta.
Dangote ya kuma bayyana cewa, da zarar sun samu danyen mai daga NNPC da aka kayyade da naira, za su ci gaba da sayar da fetur da naira. Kamfanin ya gode wa al’umma da fahimtar da suka bayar a wannan lokaci mai wahala.
Wannan dakatarwar ta jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan kasuwa da masu amfani da man fetur a Najeriya, inda ake fargabar tasirin wannan mataki ga kasuwar mai a cikin ƙasar.