
Gamayyar jam’iyyun siyasa ta ƙasa (CUPP) ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi fatali da jam’iyyar APC a zaben 2027. Wannan kira ya biyo bayan kisan manoma 40 da aka yi a jihar Borno, wanda CUPP ta zargi gwamnati da gazawa wajen kare rayukan al’umma.
CUPP ta bayyana damuwarta game da karuwar rashin tsaro a Najeriya, inda ta ce idan APC ta ci gaba da mulki, ƙasar na fuskantar mummunan sakamako. Mai magana da yawun CUPP, Kwamared Mark Adebayo, ya yi gargadin cewa lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su farka da wannan lamari a zaben da ke tafe.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan ta’adda da suka jawo uuuuuuo rayuka da dukiyoyi, tana mai jaddada cewa akwai bukatar gaggawa a cikin tsarin tsaron ƙasa. Ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.
CUPP ta bayyana cewa, duk da biliyoyin Naira da aka kashe a fannin yaki da ta’addanci, babu wata gagarumar nasara da aka samu. Ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya, tana mai jaddada cewa, “ba za a iya ci gaba da zama ba tare da tsaro ba.”
Matan CUPP sun yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin na jihar Borno, tare da fatan cewa gwamnati za ta dauki matakan da suka dace don ganin an magance wannan babbar matsala.