Cire Tallafin Fetur Ya Fara Haifar da Sauƙi ga Talakawa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cire tallafin man fetur na da tasiri mai kyau a kan rayuwar talakawa a Najeriya. Hadimin Shugaban Kasa, Abdullahi Tanko Yakasai, ya bayyana hakan ne yayin rabon kayan tallafi ga ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano.

Yakasai ya ce matakin cire tallafin fetur ya jawo sauƙin rayuwa a cikin al’umma, duk da cewa an fuskanci wasu kalubale tun bayan wannan sauyi. Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na aiki tukuru domin tabbatar da cewa marasa ƙarfi suna samun tallafi da goyon baya daga gwamnatin.

A cewarsa, wannan mataki na cire tallafin fetur na da nufin adana kuɗaɗe da za a yi amfani da su wajen aiwatar da manyan ayyuka a fannonin lafiya, noma, da sauran sassa masu mahimmanci. Yakasai ya nuna cewa gwamnatin na son tabbatar da cewa kowane bangare na al’umma ya amfana daga ci gaban kasa.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da goyon bayan gwamnati a wannan sabon tsari, wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar talakawa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa..