Cece-kuce a Kano: Gwamnati Ta Mayar da Martani Ga Tsohon Sakatare Bichi, Ta Bayyana Dalilin Korarsa

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga zarge-zargen da tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Abdullahi Baffa Bichi ya yi mata, inda ta ce zarge-zargen nasa ba su da tushe balle makama.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Garba Waiya, ya ce gwamnati ta yi takaicin kalaman Bichi, yana mai cewa sun cika da kiyayya ta siyasa. Ya ƙalubalanci Bichi da ya gabatar da hujjoji kan zargin rashawa da ya yi wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Waiya ya ce gwamnatin Kano tana da cikakken tsari na gaskiya da riƙon amana, kuma ba za ta lamunci zarge-zarge marasa tushe ba. Ya kuma bayyana ainihin dalilin da ya sa aka kori Bichi, inda ya ce ba wai rashin lafiya ba ne kawai kamar yadda aka bayyana a baya.

“Mun ɓoye ainihin dalilin da ya sa aka kore shi, muka ce matsalar rashin lafiya ne, saboda mutuntawa. Amma ya kamata a sani cewa cire shi ba kawai saboda rashin lafiya aka yi ba,” in ji Waiya.

Gwamnatin Kano ta bukaci jama’a da su yi watsi da zarge-zargen Bichi, tana mai cewa an yi su ne don ɓata mata suna da kuma karkatar da hankali daga ainihin ayyukan raya jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *