
Zargin Karya: Reno Omokri Ya Kafa Hujja Kan Nasir El-Rufai a Jihar Kaduna
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi zargin cewa Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, na yada ƙarya game da matakan tsaron da gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka a jihar.Omokri ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kashe shugabannin ‘yan bindiga fiye da 14, abin da ya kawo zaman lafiya a yankin Arewacin Najeriya. Ya zargi El-Rufai da kokarin kawar da al'ummar Kiristoci daga Kudancin Kaduna, amma wannan shiri na sa ya ci tura.A cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Omokri ya bayyana cewa El-Rufai yana cikin damuwa saboda gazawarsa wajen yin tasiri kan magajinsa, Sanata Uba Sani, da harkokin mulkin Kaduna. Ya yi zargin cewa a tsawon shekaru takwas da El-Rufai ya mulki Kaduna, ba a kama ko kashe wani shugaban ‘yan bindiga ba.Omokri ya jaddada cewa a karkashin gwamnati...