
Jigon APC Ya Kaddamar da Aikin Sulhunta Manyan Ƴan Siyasa a Kano
Abdulsalam Abdulkarim Zaura, jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, ya bayyana aniyarsa ta sasanta manyan ƴan siyasa uku: Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje, da Ibrahim Shekarau. Wannan shiri na sulhunta ya biyo bayan damuwa da ya bayyana kan rashin haɗin kai tsakanin wadannan jiga-jigan siyasar.Zaura, wanda tsohon ɗan takarar sanatan APC ne, ya ce sasanta shugabannin siyasar na da matukar muhimmanci wajen canza yanayin siyasar jihar daga adawa zuwa ci gaba. Ya bayyana cewa, "Siyasar adawa da ake yi a Kano a halin yanzu ba ta da wani amfani. A shirye nake na yi aiki don ganin cewa shugabannin siyasar mu guda uku sun haɗa kai."Ya kara da cewa, haɗa kan waɗannan shugabannin zai tabbatar da cewa Kano ta samu ci gaba mai dorewa, kamar yadda wasu jihohi, musamman Legas, suka yi. Zaura ya n...