
APC Ta Shirya Ba Tinubu da Ganduje Tikitin Tazarce a Zaben 2027
Jam'iyyar APC ta fara shirin tunkarar babban zaben 2027 tare da niyyar ba wa shugaba Bola Tinubu da sauran jiga-jigan jam'iyyar tikitin tazarce. Wannan mataki na APC na zuwa ne a lokacin da siyasa ke kara zafi a Najeriya, inda jam'iyyar ke fuskantar kalubale da kuma bukatar tabbatar da zaman lafiya a tsakaninta.Rahotanni sun nuna cewa manyan shugabannin APC sun amince da wannan shiri a wani taron da aka gudanar, wanda zai taimaka wajen gujewa rikicin shari’a da fusatattun 'yan jam'iyya. Haka zalika, an bayyana cewa wannan shiri na bayar da tikitin tazarce yana daga cikin dalilan da suka sa wasu manyan 'yan majalisar adawa suka sauya sheka zuwa APC.Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki zai ba da damar gwamnoni su yanke hukunci kan wanda zai tsaya takara a jihohinsu, w...