
Yan Adawa Sun Fara Wani Shirin Ture Tinubu a Zaɓen 2027
Jam'iyyar Labour, wacce ta samu nasarar shiga sahun manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya, ta fara shirin tunkarar zaɓen 2027. Jam'iyyar ta yi wani taro na musamman domin fara shirin kifar da gwamnatin APC a zaɓen shekarar 2027.A yayin taron, wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban tattaro jama'a na jam'iyyar LP, Marcel Ngogbehi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun shiga Aso Rock Villa a 2027.Ngogbehi ya ce jam'iyyar LP za ta mayar da hankali kan neman goyon bayan yan ƙasa a yanzu, domin samun nasara a zaɓen 2027. Ya ce za su hada kan al'umma, domin samun karɓuwa a sassan Najeriya."Mun shirya wannan taron ne domin neman yadda za mu hada kai mu samar da mafita ga matsalolin Najeriya," in ji Ngogbehi. "Ina kira a gare ku da ku kulla alaka da mutane, ku sanar da su m...