
Jam’iyyar APC Ta Gargadi wani Gwamnan Kan Tsoma Baki a Harkokinta
Jam'iyyar APC ta gargadi gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara, kan zargin tsoma baki a harkokin jam'iyyar. Shugaban APC na jihar, Cif Tony Okocha, ya zargi Fubara da daukar nauyin wasu shari'u da jam'iyyar ke fuskanta, yana mai cewa ya kamata ya daina wannan hali.Okocha ya yi ikirarin cewa gwamnan na kokarin bata sunan jam'iyyar APC a jihar, yana mai cewa: "Ka daina shiga harkokinmu, ko kuma za mu dauki mataki." Ya kuma tambayi dalilin da ya sa gwamnan ba zai yi amfani da karfinsa wajen gyara jam'iyyar PDP ba, maimakon tsoma baki cikin harkokin APC.Gwamna Fubara, a martaninsa, ya ce ba shi da lokacin tsoma baki cikin harkokin APC, yana mai bayyana kansa a matsayin cikakken dan jam'iyyar PDP. Mai ba shi shawara, Jerry Omatsogunwa, ya ce gwamnan yana halartar taron jam'iyyar PDP kuma yana ...