
Yarjejeniyar siyasa tsakanin Kwankwaso da Atiku da Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ya cimma tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi kan wa'adin mulki. A yayin tattaunawa da sashen Hausa na RFI, Kwankwaso ya bayyana cewa maganar ta ƙona masa rai, inda ya ce dattawa ba su kamata su faɗi abubuwan da ba su yi ba.Kwankwaso ya ce labarai sun bayyana cewa ɓangaren Atiku Abubakar ne ke yaɗa wannan maganar, suna yi wa malamai da shugabanni magana kan yarjejeniya da ba ta taba faruwa ba. Ya ƙara da cewa, "Wannan magana ta ƙona mani rai matuƙa, a ce dattawa suna ƙarya."Ya musanta jita-jitar cewa sun yi yarjejeniya kan karba-karba, inda ya ce, "An gaya musu wai na amince cewa Atiku zai yi shekara huɗu, ni ma zan yi hudu, wancan shi kuma Peter Obi ya yi sh...