
APC Ta Karyata Kalaman Peter Obi, Ta Zarge Shi da Son Jawo Tashin Hankali
Jam'iyyar APC ta yi zazzafan martani ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, bisa ga shawarwarin da ya bayar na sukar gwamnatin Bola Tinubu. Obi ya yi kira ga Tinubu da ya rika neman lafiya a asibitocin Najeriya maimakon tafiya kasashen waje.APC ta zargi Obi da kokarin jawo wa gwamnatin tarayya bakin jini, duk da kokarin da ake yi na magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta. Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Felix Morka, sakataren yada labaranta na jam'iyyar, wanda ya ce kalaman Obi suna dauke da harzuka da ke iya jawo tashin hankali a tsakanin al'umma.Obi ya ce akwai bukatar Tinubu ya daina shan wahala wajen neman lafiya a waje, yana mai cewa hakan na nuna cewa gwamnatin na fama da matsaloli. APC ta karyata ikirarin Obi na cewa gwamnatin Tinubu ta gaza magance matsalolin tatt...