
Hon. Kofa: APC a Kano Za Ta Sha Kasa a Zaben 2027
Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ba za ta yi tasiri a zaben 2027 ba. Kofa, wanda ke cikin jam'iyyar NNPP, ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake tattaunawa game da rikice-rikicen da ke faruwa a cikin APC.A cewar Kofa, shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, zai fitar da dan takara, amma hakan ba zai kawo canji mai kyau ba, ganin cewa akwai rigingimu da suka hana jam'iyyar ci gaba. Ya zargi wasu daga cikin manyan APC da hada hannu wajen rashin nasarar takarar dan gidan Ganduje a zaben 2023.Hon. Kofa ya bayyana cewa adawa da tafiyar Kwankwasiyya na daga cikin abubuwan da ke haifar da cakwakiya a siyasar Kano. Ya ce idan ana so jam'iyyar ta yi nasara, dole ne a magance wadannan ...