Mijin Senator Natasha Ya Bayyana Matsayinsa Kan Zargin Akpabio
Mijin Senator Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Uduaghan, ya yi magana kan zargin da matarsa ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na aikata abubuwan da ba su dace ba. Uduaghan, wanda shima babban mutum ne a masarautar Warri a Jihar Delta, ya bayyana cewa matar tasa ta bayyana masa duk abubuwan da suka faru a tsakaninta da Akpabio.A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, Uduaghan ya ce ya yi ƙoƙarin shawo kan al'amarin cikin ladabi da girmamawa, tare da fatan samun sulhu. Ya ce ya yi tunanin Akpabio aboki Kuma Dan uwa, don haka ya nemi ganawa da shi don tattauna damuwar matarsa.Uduaghan ya ce, “Matar ta bayyana mini duk wani abu da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, wanda na dauka a matsayin aboki Kuma Dan uwa. Na yi ƙoƙarin magance al'amarin da kyau da hakuri, sabod...








