Majalisar Dattawa Ta Gano Mafita kan Ayyukan Yan Ta’addan Lakurawa a Jihohi
Daga Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta gudanar da zama inda ta bayar da shawarar cewa sojoji su haɗa kai da al'ummar yankunan da ke fama da hare-haren kungiyar yan ta'addan Lakurawa. Wannan shawarar ta biyo bayan mummunan hari da ƴan kungiyar suka kai a kauyen Mera a jihar Kebbi, wanda ya jawo asarar rayuka da dama.
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai na gaggawa don kawo karshen ayyukan kungiyar Lakurawa kafin ta mamaye sassan Arewa. Sanata Yahaya Abdullahi, daga Kebbi ta Arewa, ya gabatar da korafi game da matsalar a zaman, wanda ya jawo hankalin sauran sanatan.
A yayin muhawara, 'yan majalisar sun yi kira ga rundunar sojojin Najeriya su yi aiki tare da mazauna yankunan da ake kai hare-hare, domin kafa tsare-tsare da za su taimaka wajen gano s...




