Gobara Ta Tashi a Asibitin Koyarwa na LAUTECH, Dukiya Mai Yawa Ta Kone
Wata mummunar gobara ta tashi a asibitin koyarwa na jami'ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso a jihar Oyo, yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Gobarar, wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, 2024, ta yi sanadiyyar lalata dukiya mai tarin yawa ta miliyoyin Naira.
Gobarar ta shafi sashin kula da ba da agajin gaggawa da hadurra na asibitin, inda ta lalata kayan ofis, littattafai, na'urorin lantarki, rufi da silin. Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe, sakamakon tsartsarin wutar lantarki daga wani ofishi.
Hukumomin asibitin sun yi gaggawar fitar da majinyata 16 daga sashin a lokacin da gobarar ta tashi, domin kaucewa asarar rayuka. Jami'in hulɗa da jama'a na asibitin, Omotayo Ogunleye, ya tabbatar da faruwar lamar...








