NNPCL Ya Bayyana Wadanda Za a Sayarwa Fetur na Matatar Port Harcourt
A yau Alhamis, Nuwamba 28, 2024— Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya bayyana cewa fetur da aka fara samarwa a matatar Port Harcourt za a sayar da shi ne kawai ga gidajen man kamfanin. Babban jami'in sadarwa na NNPCL, Olufemi Soneye, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a fara sayar da fetur mai yawa ba, kuma ba a buɗe wajen sayarwa a halin yanzu.Olufemi Soneye ya ce: "Har yanzu ba mu fara sayar da fetur mai yawa ba, kuma har yanzu ba mu buɗe wajen saya ba yayin da muke ci gaba da kammala matakan da suka dace.""A halin yanzu, fetur da muke sayarwa wanda muka sayo ne daga matatar Dangote."Matatar man Port Harcourt ta kasance cikin yanayi mai wahala na rashin aiki na dogon lokaci kafin a fara aikin tace ɗanyen mai. Wannan ya sa aka samu jinkiri a cikin samar da fetur, wanda ya shafi kasuwar man...








