
Hukumar EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja
Daga babban birnin Tarayya Abuja: Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2024, a hedkwatar hukumar da ke Abuja. Wannan mataki na hukumar ya biyo bayan zarginsa da aikata laifuka da suka shafi cin hanci da rashawa.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kama Yahaya Bello ga manema labarai, inda ya ce dakarun hukumar ne suka gudanar da aikin. Oyewale ya bayyana cewa, "Eh gaskiya ne, muna tsare da shi a hannun mu yanzu haka."
Yahaya Bello, wanda ya kasance gwamnan jihar Kogi, ya tura tawagar lauyoyi zuwa ofishin EFCC domin amsa gayatar da aka masa. An zarge shi da karkatar da kuɗaɗen jama'a har naira biliyan 80.2. Wannan lamari ya jawo hankalin jama'a da dama, tare da sa s...