Shugaba Tinubu Ya Fadi Amfanin da Cire Tallafin Man Fetur Ya Yi Wa Najeriya
Lahadi, Disamba 01, 2024 Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar cire tallafin man fetur, yana mai jaddada cewa wannan mataki ya zama wajibi domin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya. A jawabinsa a wajen taron yaye ɗalibai karo na 34 da 35 na jami'ar Fasaha ta tarayya dake Akure, Tinubu ya yi tsokaci kan yadda cire tallafin zai taimaka wajen inganta yanayin tattalin arzikin ƙasar.Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ba ya nufin azabtar da ƴan Najeriya, amma yana da nufin ceto ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki. Ya ce:"Idan ba a cire tallafin ba, tattalin arzikin Najeriya zai durƙushe. Wannan mataki na cire tallafi yana nufin ceto al’umma daga halin rashin tabbas da aka tsinci kanta."Shugaban ƙasa ya bayyana cewa cire tallafin man fetur y...








