Kudirin Haraji: Lauya Ya Fallasa Babban Burin Legas da Aka Tabbatar kan Kudirin
Fitaccen lauya, Barista Bulama Bukarti, ya bayyana gagarumin illar da kudirin harajin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar zai yi ga yankin Arewa. Ya ce wannan tsarin haraji ba zai yi wa jihohin Arewa da dama ba, kuma an yi zargin cewa wannan yana daga cikin kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi don tabbatar da muradun jihar Legas.Barista Bukarti ya yi wannan bayani ne a cikin shirin Fashin Baki, inda ya bayyana cewa kudirin harajin da aka gabatar yana da nufin amfanin jihohin da suke da karfin tattalin arziki, kamar Legas da Ribas, yayin da sauran jihohi, musamman na Arewa, zasu fuskanci matsaloli.Lauyan ya bayyana cewa idan kudirin ya tabbata, jihohin Arewa kamar Bauchi, Yobe, da Jigawa ba za su iya biyan ma'aikatansu albashi ba. Wannan yana nufin cewa kudirin harajin zai jefa al'um...








