Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Gwamnan Jigawa
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, a ranar Juma'a. Ziyarar ta'aziyyar ta biyo bayan rasuwar mahaifiyar gwamnan, Hajiya Maryam, da ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi, wanda ya rasu a wani hatsarin mota.Sanata Lawan ya bayyana cewa rashin ɗan uwa yana da matuƙar ciwo, musamman ma idan mutum ya rasa mahaifiya da ɗa a lokaci guda. Ya roki Allah ya ba gwamnan karfin gwiwa da juriyar wannan rashi mai raɗaɗi.A lokacin ziyarar, Sanata Lawan ya bayyana cewa: "Rasuwar 'yan uwa ba zato ba tsammani abu ne mai raɗaɗi, amma rashin uwa da ɗa a lokaci guda ya wuce duk yadda za a misalta." Ya kuma bayyana cewa Hajiya Maryam ta kasance mai kishin addini da tallafawa mutane a cikin al'umma.Daga cikin wadanda suka jajantawa g...








